Thursday 31 March 2022

Wani matashi yalashi takobin siyawa Eng Dr Rabi'u musa Kwankwaso Form din takara a jam'iya me alamar kayan marmari

 Zan Sayawa Kwankwaso Form Din Takarar Shugaban Kasa ~''Dr Ahmad Isah''


Shugaban gidan radio human right fm dake Abuja ya lashi takobin sayawa Sanata Eng Dr Rabi'u Musa Kwankwaso form din tsayawa takarar shugaban kasa domin yasamu damar tsawa takarar shugaban kasa a shekara ta


2023


''Dr Ahmad Isah'' yabayyana hakanne ta cikin shirin (Briket Family)da yagabata a safiyar yau yace dalilin da yasa yadau wannan alkawari shine yagama nazarinsa baiga wanda yake amfanar da dan talaka ba da kaunar dan talaka kamar kwankwaso


Yace hakanne yasa yadau wannan alkawari.

Ankamo wata budurwa datayi tattaki daga jihar bauchi zuwa birnin tarayya abuja

Ankamo Amira Ahmad mai shekaru 22 da fara tattaki daga Bauchi zuwa Abuja domin nuna goyon bayanta ga dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC Farouq Mustapha da kuma karrama 'yar dan takarar kan shiga cikin talakawa da yafi a taron da jam'iyyar APC ta gurdanar a Abuja.


Dan takarar gwamnan Farouq Mustapha, ya bada umurnin a dakatar da ita, ta koma gida zai biya mata kudin jirgi ko na mota domin taje Abuja ta sameshi duba da halin rashin tsaron da ake ciki.


Yanzu dan takarar ya bayyana a shafin sa na Facebook da cewa an samo nasarar kamo ta a garin Jos.


Ga abunda ya rubuta kamar haka; "A safiyar yau na samu labarin wannan baiwar Allah Amira Ahmad Bauchi ta fara tattaki zuwa Abuja domin karrama ni da iyalina. Cikin gaggawa na sanya Daraktan Kamfen dina ya bita, inda ya sameta a Jos. Ya dauketa cikin koshin lafiya kuma ya maidata gida wajen iyalinta".


"Ina godiya ga Amira kuma zan gaiyaceta zuwa zama na musamman tare da iyalina anan Bauchi".

"Kamar yanda muke fadi tashi wajen inganta rayuwar iyalanmu, nauyi ne akan mu mu inganta rayuwar magoya bayanmu".

Rahoto daga daily Nigeria Hausa


Tuesday 29 March 2022

KWANKWASO YAFICE DAGA JAM'IYYAR PDP ME ALAMAR LEMA

  Ayau talatane 29th gawatan march jagoran ɗariƙar kwankwasiyya Tsohon Gwamnan Kano hawa biyu kuma sohon sanatan kano ta tsakiya injiya Dr Rabi'u Musa Kwankwaso yasanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP me alamar lema tare da komawa sabuwar jam'iyya me alamar kayan marmri,sanarwar tafutone daga mataimakinsa aɓangare kafofin sadarwa na yanar gizo-gizo Hon.Saifullahi Hassan ta shafinsa na sadarwa bangaren facebook.

Ash-shifa Yunus AYD


Sakon tuni ga yan najeriya daga sanata shehu sanii

 Ikon Allah,Babu irin zagin da ban sha ba,Babu irin cin mutuncin da ban gani ba a lokacin da muka fara magana kan rashin tsaro a Arewacin Na...