Thursday 31 March 2022

Ankamo wata budurwa datayi tattaki daga jihar bauchi zuwa birnin tarayya abuja

Ankamo Amira Ahmad mai shekaru 22 da fara tattaki daga Bauchi zuwa Abuja domin nuna goyon bayanta ga dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC Farouq Mustapha da kuma karrama 'yar dan takarar kan shiga cikin talakawa da yafi a taron da jam'iyyar APC ta gurdanar a Abuja.


Dan takarar gwamnan Farouq Mustapha, ya bada umurnin a dakatar da ita, ta koma gida zai biya mata kudin jirgi ko na mota domin taje Abuja ta sameshi duba da halin rashin tsaron da ake ciki.


Yanzu dan takarar ya bayyana a shafin sa na Facebook da cewa an samo nasarar kamo ta a garin Jos.


Ga abunda ya rubuta kamar haka; "A safiyar yau na samu labarin wannan baiwar Allah Amira Ahmad Bauchi ta fara tattaki zuwa Abuja domin karrama ni da iyalina. Cikin gaggawa na sanya Daraktan Kamfen dina ya bita, inda ya sameta a Jos. Ya dauketa cikin koshin lafiya kuma ya maidata gida wajen iyalinta".


"Ina godiya ga Amira kuma zan gaiyaceta zuwa zama na musamman tare da iyalina anan Bauchi".

"Kamar yanda muke fadi tashi wajen inganta rayuwar iyalanmu, nauyi ne akan mu mu inganta rayuwar magoya bayanmu".

Rahoto daga daily Nigeria Hausa


No comments:

Post a Comment

Sakon tuni ga yan najeriya daga sanata shehu sanii

 Ikon Allah,Babu irin zagin da ban sha ba,Babu irin cin mutuncin da ban gani ba a lokacin da muka fara magana kan rashin tsaro a Arewacin Na...