Sunday 3 April 2022

Hukumar hizba a jihar kano tayi gargaɗi ga musulman da suke cin abinci tsakiyar rana acikin watan ramadan

 Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ci alwashin saka kafar wando ɗaya da matasa Musulmai da su ke ƙin yin azumin watan Ramadan.


A wani sakon murya ta kafar WhatsApp da ya tura wa manema labarai a yau Asabar, Babban Kwamandan Hukumar, Muhammad Harun Ibn-Sina ya ce Hukumar ba za su saurara wa masu karya shari’ar Muslunci da gangan ba.


A cewar sa, duk wanda a ka samu musulmi ya na cin abinci da rana ba tare da wata larura ba to zai gamu da fushin Shari’a.


Ya kuma kara da cewa hukumar ba za ta zuwa ido ta ga a na aikata baɗala a watan Ramadan da ma bayan sa ta ƙyale ba, inda ya ce dole ne ta yi aikinta na horo da kyakkyawan aiki da kuma gani da mummuna.


Ibn-Sina ya kuma taya musulmai a faɗin jihar da ƙasa baki ɗaya murnar zagayowar wata mai alfarma, inda ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun Ya kuma kawo zaman lafiya da arziki a ƙasar nan.



No comments:

Post a Comment

Sakon tuni ga yan najeriya daga sanata shehu sanii

 Ikon Allah,Babu irin zagin da ban sha ba,Babu irin cin mutuncin da ban gani ba a lokacin da muka fara magana kan rashin tsaro a Arewacin Na...