Friday 1 April 2022

TIRKASHI,WASU FUSATATTUN MATASA SUN KONA MOTOCIN YAKIN NEMAN ZABEN SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA BISA ZARGINSA DA SA HANNU ACIKIN HARKAR RASHIN TSARON JIHAR

Wata sabuwa.....


Ana Zargin Sakataran Gwamnatin Jihar Katsina Kuma Dan Takarar Gwamna Dr. Mustapha Inuwa, Da Daukar Nauyin ‘Yan Ta’addan Dake Kai Hare-hare A Jihar Katsina


A jiya ranar Alhamis ne wasu fusatattun Matasa suka ƙone motar yankin Neman zaben Sakataren gwamnatin Jihar Katsina Kuma ɗan takaran gwamnan jihar a garin Charanci.


Lamarin ya auku ne a daida lokacin da a yarin motar Magoya bayan Sakataren gwamnatin suka zo wucewa ta garin na Charanci kan hanyar su ta zuwa karamar Hukumar Kankia domin halartar taron bayar da Tuta ga ƴan takarar Chiyamomi 34 na jam’iyyar APC.


Mustapha Inuwa, a baya baya ansha zarginsa da daukar nauyin ‘yan ta’addan dake kai hare hare a Jihar Katsina lamarin daya karyata Kuma yayi Bayanin alakarsa da ‘yan ta’addan Yan bindiga dake fa’din jihar ta Katsina.


A ranar 16 ga watan maris daya gabata ne sakataren Gwamnatin Jihar ta Katsina ya tara taron Yan jarida Kuma ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar Gwamnan jihar Katsina Kuma a lokacin yayi Bayanin alakarsa da ‘yan bindigar da ake Zargin sa a fadin jihar.


A lokacin da yake mayar da martani sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa, ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da ƴan bindiga kamar yadda ake ta raɗe-raɗin cewa wai yana da alakar kud da kud da ƴan bindiga a jihar, yace shima ya ɗanɗana azabar su kamar sauran mutane.


Inuwa wanda aka nada sakataren gwamnatin Katsina tun bayan zaman Aminu Masari gwamna ya bayyana aniyarsa na yin takarar gwamnan jihar a 2023.


Mutane da dama na zargin Inuwa da hada hannu da ‘yan bindiga da hakan ya sa matasa suka kona gidan sa dake karamar hukumar Danmusa a shekarar 2019.


Danmusa na daga cikin kananan hukumomin jihar Katsina da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga.


Ni ma na yi fama da hare-haren ‘yan bindiga, a cewar shi;


Yayin da yake ganawa da manema labarai ranar Laraba a lokacin da yake bayyana aniyar sa ta yin takarar gwamnan jihar Inuwa ya ba shi da alaka da ƴan bindiga fomin shima yayi fama da azabar da suka rika gallaza wa mutane, bai kubuta ba.


Ya ce sau biyu yana sadaukar da ransa domin a samu daidaituwa tsakanin gwamnati da ƴan bindiga kawai domin a samu zaman lafiya a jihar.


“A kan babur na yi dogon tafiya cikin gungurmin daji domin kawai a samu zaman lafiya. Na yadda su yi garkuwa da ni domin shugaban su ya je ya tattauna da gwamnati


“Na yi haka ne domin a samu zaman lafiya a jihar, kuma saboda na yadda da gwamna da kokarin da gwamnati ke yi don kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga a jihar.


“Ko su ‘yan bindigan sai da suka yi mamakin gani na a wannan lokacin.


Da yake bayanin yadda ya yi fama da hare-haren ‘yan bindiga Inuwa ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da babban wansa, ‘yar dan uwansa da abokinsa a Danmusa da dole sai da suka biya kudin fansa kafin aka sake su.


“Mukan zauna da ƴan bindigan da suka tuba duk bayan sati biyu domin tattaunawa da yadda za mu sasanta da sauran ‘yan bindigan.


“Sannan lokacin da maganan sasantawa da gwamnati ya rushe wasu daga cikin tubabbun ‘yan bindigan sun koma ruwa suna kai wa mutane hari.

No comments:

Post a Comment

Sakon tuni ga yan najeriya daga sanata shehu sanii

 Ikon Allah,Babu irin zagin da ban sha ba,Babu irin cin mutuncin da ban gani ba a lokacin da muka fara magana kan rashin tsaro a Arewacin Na...