Saturday 9 April 2022

Sakon tuni ga yan najeriya daga sanata shehu sanii

 Ikon Allah,Babu irin zagin da ban sha ba,Babu irin cin mutuncin da ban gani ba a lokacin da muka fara magana kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya.Wai yanzu su da kansu suke fadi bayan abubuwa sun tabarbare gaba daya.

Wanda suka zage mu Mun barsu da Allah.


2023: Ni zan fara yin Mataimakiyar Shugaban Ƙasa -- Yahaya Bello Gwamna Kogi State

 2023: Ni zan fara yin Mataimakiyar Shugaban Ƙasa -- Yahaya Bello



Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce zai ɗauki mace ta yi masa mataimakiya idan jam'iyar APC ta tsaida shi takarar shugaban ƙasa a 2023.


Bello ya baiyana hakan ne a wani taron karawa juna sani da ƴan jarida masu rahoton labaran siyasa da na kotu a jiya Juma'a a Abuja.


A cewar Bello, zai baiwa mata muhimmanci idan har a ka bashi dama ya zaɓi wanda zai yi takara da shi.


Gwamnan ya ce ya na da burin yin gwamnati da za ta tafi da kowa, musamman mata, matasa da masu buƙata ta musamman.


Ya ƙara da cewa haka ya ke gudanar da mulkinsa a Kogi in da bai bar kowa ba wajen tafiyar da gwamnatinsa.


Bello ya ƙara da cewa idan ya samu dama, zai samar da tallafi ga matasa da mata domin bunƙasa tattalin arziki.

Tuesday 5 April 2022

MUBARAK BALA YA AMSA LAIFINSA A KOTU

 Mubarak Bala ya amsa laifin aikata sabo a gaban kotu


Wata babbar kotu a Kano ta sake aikewa da Mubakar Bala zuwa gidan gyaran hali, saboda ci gaba da tsare rayuwarsa da kuma gazawar lauyoyinsa na gabatar wa kotun da cikakaken takardun da za su tabbatar mata cewar yana fama da rashin lafiya.


An karanto ma M


ubarak Bala caji 14 da ake tuhumarsa a kai na yin sabo.


Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, wadanda yayi kalaman batanci ga addinin Musulunci.


Ya amsa dukkan caji 14 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.


Ganin haka sai lauyansa ya roki kotun ta ba shi damar ganawa da wanda yake wakiltar, wato Mubarak Bala, kuma bayan ta amince, ya yi kokarin nuna ma sa tasirin cewa ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa.


Amma bayan da lauyan ya sanar da kotun cewa Mubarak Bala na son sauya amsar da ya bayar a gaban kotun, sai alkalin ya sake tambayar wanda ake tuhumar ko haka lamarin yake.


Mubarak Bala ya sanar da kotun cewa ba zai sauya amsa laifinsa da ya yi a gaban kotun ba.


Alkali kotun ya tambaye shi ko ya fahimci nauyin abubuwan da yake cewa, kuma wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya fahimci komai.


Ya kara da cewa babu wanda ya tursasa masa don ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa. Sannan ya ce babu wanda yayi masa wani alkawari, ko ya sanya masa wani ra’ayi, sai dai ya bukaci kotun ta yi masa sassauci da kuma adalci.


Wakilin BBC da ke kotun ya ce kotun na ci gaba da sauraron shari'ar.


Tushe: BBC Hausa

Monday 4 April 2022

Cire sheikh nuru Khalid daga limanci ba abinda zai rageshi dashi sedai samun daukaka danasara arayuwa

 Sheikh Nura Khalid


cire shi daga limanci babu abinda zai kara masa sai nasara 


Yanzu na fahinci hikima wasu malamai da suke nemo taimako daga kasa shen waje ko daga wasu mutane abokai ko dalibai su gina musu makaranta da masallaci hakan yana basu enci fadin gaskiya ba tare da jin tsoron makircin yan komati ba 


Hassada da bakin ciki itace takesa yan komati su cire malami daga shugabanci  

Duk inda kaga an cire malami daga shugabanci akwai wani  alkhairi daba'a so malamin yaci gaba da samu 


masallacin Apo shine masallaci na biyu Abuja dake unguwar gidajen yan'majalisa tarraya 


Sheikh Nura khalil shine limamin masallacin na farko tun bayan kammala gini masallacin malam musa limamin masallacin National mosque shine ya nada shi limamcin masallacin


Tare dani aka bude masallacin  sheikh Nura khalil yayi kokari sosai wajen raya masallacin da karantarwa ta ilimi mutunne jajirtacce wajen gina al,umma  tun lokacin da aka bawa malam limanci masallacin wasu daga cikin malamai suke masa hassada sunaso suga bayansa  


yanzu don yayi magana kada talaka ya fito yayi zabe matukar ba'a daina kashe  shi ba,meye laifin malam akan wannan magana ba gaskiya ya fada ba ? 


Wannan magana tana tayarwa da duk wani dan' siyasa hankali mai son kujerar mulki,basa son suji ance kada mutane sufito suyi zabe,sai kaji wasu masu wayo daga cikinsu sun fara fakewa da magana addini ko kabilanci idan baku fito Kukayi zabe ba makiyanku  sune zasu samu dama akanku su mulkeku su dinga kashe ku, irin wannan kalmomi dasu suke amfani wajen mulkar jama'a. 


Kullun ina tambaya kaina danamu suka samu mulki mai sukayi wajen kare martabar addini da rayukan jama'a ?


Wanda suka cire malaman daga limanci  babu wata martaba da zasu samu daga wajen gobnati


Malan yana da sabanin fahinta tsakaninsa da wasu malamai  akan wasu fahintoci da yake dasu 

Irinsu:- 

*Taron maulidi  

*Musulmi su daina kafirta juna

*Hadin kai tsakanin addinai musulmi da Kiristoci su hada kai su zauna lafiya su daina kashe junansu 


Irin wannan fahinta da malan yake da ita tasa wasu suna munana masa zato wasu kuma suna kyautata masa zaton alkhairi 


ALLAH ka fahintar damu addini kadauwamar

 damu akan shiriya



Daga malam Kabiru Abdullahi

Sunday 3 April 2022

Hukumar hizba a jihar kano tayi gargaɗi ga musulman da suke cin abinci tsakiyar rana acikin watan ramadan

 Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ci alwashin saka kafar wando ɗaya da matasa Musulmai da su ke ƙin yin azumin watan Ramadan.


A wani sakon murya ta kafar WhatsApp da ya tura wa manema labarai a yau Asabar, Babban Kwamandan Hukumar, Muhammad Harun Ibn-Sina ya ce Hukumar ba za su saurara wa masu karya shari’ar Muslunci da gangan ba.


A cewar sa, duk wanda a ka samu musulmi ya na cin abinci da rana ba tare da wata larura ba to zai gamu da fushin Shari’a.


Ya kuma kara da cewa hukumar ba za ta zuwa ido ta ga a na aikata baɗala a watan Ramadan da ma bayan sa ta ƙyale ba, inda ya ce dole ne ta yi aikinta na horo da kyakkyawan aiki da kuma gani da mummuna.


Ibn-Sina ya kuma taya musulmai a faɗin jihar da ƙasa baki ɗaya murnar zagayowar wata mai alfarma, inda ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun Ya kuma kawo zaman lafiya da arziki a ƙasar nan.



Khalifan tijjaniyya sarki sanusi lamiɗo sanusi yaba shugaba buhari muhimmiyar shawar


 Sarki Sanusi Lamido Sanusi

Muhimmiyar Shawara Ga shugaba

Buhari Domin Ceto Kasarmu Nijeriya.

*Ya Kamata Canji Ya Soma Daga

Majalisa


_ Sanata na karbar Naira Miliyan

36,000,000 kowane wata.

Idan aka raba gida biyu yana karbar

Naira Miliyan 18,000,000, ragowar

*Naira Miliyan 18,000,000 za a iya

amfani da su wajen daukar 'yan

Nijeriya 200 aiki kowa ya rika daukar

albashin Naira Dubu 90,000 kowane

wata.*


Idan aka yi mutum 200 sau adadin

Sanatocin mu 109 hakan na nufin za

a dauki 'yan Nijeriya *dubu 21800

aiki *


A takaice 'yan Nijeriya 200 za su iya

rayuwa a wadace da rabin albashin

Sanata na kowane wata.

*Dan Majalisar Wakilai na karbar

albashin Naira Miliyan 25,000,000

kowane wata.*


Idan aka raba albashin gida biyu ya

zama Naira Miliyan 12.5million a

wata. Ragowar *Naira Miliyan 12.5

za ta isa a dauki 'yan Nijeriya 135

aiki su rika daukar albashin Naira

dubu 92,500 a wata*.

'Yan Nijeriya 135 sau adadin yawan

'yan Majalisar Wakilai 360, hakan na

nufin za a dauki 'yan Nijeriya *dubu

48600 aiki*.

Saturday 2 April 2022

An Dauki Nauyin Karatun Budurwar Da Ta Fara Tattaki Daga Bauchi Zuwa Abuja A Kafa, Tare Da Bata Makudan Kudade

 DA DUMI-DUMINTA: An Dauki Nauyin Karatun Budurwar Da Ta Fara Tattaki Daga Bauchi Zuwa Abuja A Kafa, Tare Da Bata Makudan Kudade


Rahoton Daily News Hausa


A yau Jumma'a Amira Ahmad ta hadu da dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a Jam'iyyar APC Farouq Mustapha a gidanshi dake jihar Bauchi.


Idan baku manta ba, a jiya Alhamis "Daily News Hausa" muka kawo muku rahoton Amira Ahmad dake zaune a jihar Bauchi inda ta fara tattaki tun daga jihar Bauchi da niyyar zuwa Abuja domin nuna goyon bayan ta ga dan takarar Gwamnan Jihar a Jam'iyyar APC Farouq Mustapha, tare da karrama 'yarshi kan namijin kokarin da tayi na shiga cikin tawagar talakawa a yayin taron Jam'iyyar da ya gudana a babban birnin Tarayya Abuja.


Dan takarar Gwamnan ya gaggauta dakatar da budurwar inda ya bada umurnin a dawo da ita gida duba da halin rashin tsaro da ake fama dashi, masu dakatar da itan, sun cimma ta a garin Jos suka dawo da ita gida.


A yau Jumma'a Amira ta hadu da dan takarar yayin ziyarar da ya kawo jihar Bauchi inda ya bata mak


udan kudad

Anzargi Gwamnatin Kano dayin katsalandan a cikin Shari'at sheikh Abdul jab bar Nasir kabara

 An zargi gwamnatin


Jihar Kano ta Abdullahi Umar Ganduje da yunkurin yin katsalandan a shari’ar da ake yi wa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara a kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke yi wa jagoranci.


A taron manema labarai da ya kira a karshen mako a Kano, Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare na Cibiyar Tallafa wa Gajiyayyu ta AGB (A Grateful Band), Injiniya Ibrahim Abdullahi Warure, ya nuna damuwa matuka a kan bayanan da ke fitowa daga bangarori daban-daban a kan kai-komon da gwamnatin Kano da abokan burminta, Malaman Maja ke yi tun daga ranar 03/03/2022 da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fara kare kansa a kan tuhume-tuhumen da ake yi masa da nufin canza akalar shari’ar zuwa wani abu na daban.


Injiniya Warure ya tabbatar da cewa, sabbin bayanan sirrin da suka samu daga majiyoyi masu tushe, sun fallasa wasu kulle-kullen da ake yi na kawo wa shari’ar cikas, ta hanyar tilasta wa Alkalin da ke shari’ar ya daure Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ko da bai same shi da wani laifi ba.


A zama biyu na baya-bayan nan da aka yi a ranar 3 da 17 ga wannan watan da muke ciki, Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya warware zare da abawa kan wasu daga cikin tuhume-tuhumen da aka yi masa, tare da gabatar da littattafai 27 da ya dogara da su, ta hanyar daukar zarge-zargen da ake masa guda takwa daya bayan daya yana warware su.


Cibiyar ta AGB, ta ce suna nuna damuwarsu ne bayan sun samu labarin irin matsin lambar da Alkalin yake fuskanta, tare da zama kashi takwas, ciki har da wanda Malaman Maja suka yi a garin Fatakwal babban birnin Jihar Rivers a kan yadda za su bullo wa shari’ar.


“Duk da yake maganar da ke gaban shari’a ba a tattauna ta, ana barin a ga me zai faru ne a kotu, amma sun nuna fargabarmu a kan kai-komin da wadanda suke son lallai sai an samu Shaikh Abduljabbar da laifi suke yi wajen ganin an tauye masa hakkokinsa da dokar kasa ta ba shi.


“Tun farko mai bai halatta kowace irin kotu ta saurari abin da mutum ya yi imani da shi a matsayin addini ko a matsayin Ubangijinsa, kamar yadda kuma ba wata kotu da take da hurumin sauraron wata kara da aka shiga da ake tuhumar wani Malami ya yi fassarar bisa fahimtarsa, ko ya koyar, ko ya tsaya a kan abin da ya fahimta sabanin abin da Malamai suke a kai.


“Kamar yadda masana shari’ar suka tabbatar kotunan Shari’a da muke da shi ba su da hurumin sauraron duk wani abu da ya shafi addini irin wannan, ikon su shi ne maganar gado, aure da sauran abubuwan da suka shafi wannan.


“Kamar yadda masana shari’ar suka tabbatar kotunan Shari’a da muke da shi ba su da hurumin sauraron duk wani abu da ya shafi addini irin wannan, ikon su shi ne maganar gado, aure da sauran abubuwan da suka shafi wannan.


“Ba wata kotu a duniya da take da halaccin tattauna abin da ya shafi imani. Wannan maganar ta Shaikh Abduljabbar ba ta kotu ba ce, ta tattaunawa ce a tsakanin Malamai, kuma su Malaman ba wanda yake da ikon ya tankwara wani Malami ya yi fahimtarsa”, in ji shi.


Daliban Shaikh Abduljabbar, wadanda suka zargi gwamnatin Kano da Malaman Maja da zama kanwa uwar gami a kan wadannan kulle-kullen ganin sun yi wa shari’ar kafar ungulu, sun nuna gamsuwarsu a kan yadda shari’ar ke tafiya, wanda Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ba shi damar kare kansa, har da gabatar da littattafai 27, bayan kuwa su suna so ne a daure shi ba tare da an ji bahsin daga bangarensa ba.


“Wannan dai ita ce damar da Shaikh Abdujabbar Nasiru Kabara ya rasa a wajen zaman titsiye da aka kira shi da mukabala da aka yi ranar 8 ga Agusta, 2021. Gangami aka yi tsakanin gwamnati da hadakar kungiyiyin Kadiriyya, Tijjaniyya, Izala da Sallafiyya sun shirya suna son daure shi ko ta halin kaka”, in ji Injiniya Ibrahim Abdullahi Warure.


Kazalika sun nuna damuwa a kan abin da daya daga cikin Lauyoyin gwamnati ya fada wa ’yan jarida bayan an fito zaman kotu na ranar 17 ga wannan watan, inda yake cewa duk wadannan littattafan da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke kafa hujja da su a gaban kotu, ba a matsayin komai suke ba a kan wannan shari’ar, domin dokar Jihar Kano ya karya.


Suka ce duk matakan da ake dauka a kan Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara tun daga watan Fabrairu, 2021 da aka rufe masa masallaci da makarantar As’habul Kahfi, sun yi hannun riga da kundin tsarin mulkin kasar nan, amma ana yin amfani da karfin mulki ne kawai ake takawa da murjewa.


Ya ba da misali da kamun da aka yi wa Barista Hashim Husaini Fagge a cikin watan Nuwamba, 2021 da nufin a rufe masa baki saboda irin yadda yake fito da asalin gaskiyar dalilin da ya sa aka kama Shaikh Abduljabbar, tare da nuna rashin dacewar umarnin da Gwamnan Abdullahi Ganduje ya bai wa Malamai a ranar Litinin 19/7/2021 na su yi hudubar sukar Shaikh Abduljabbar a kan mumbarorinsu.


Injiniya Ibrahim Warure, ya yi kira ga kungiyoyin Lauyoyi na kasa da kasa da ta Nijeriya da sauran kungoyoyin farar hula da na masu rajin kare hakkin bil’adama, su sa ido sosai wajen ganin an yi wa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara adalci a kan tuhume-tuhumen da ake yi masa.


Daga karshe, Injiniya Ibrahim Warure, ya yi fatan wannan shari’ar da ake yi wa Shaikh Abduljabbar za ta bude sabon shafi wajen hanyar dakile duk wani zalunci da rashin adalcin da za a yi wani a kan imaninsa, ko kuma ’yancin fadar albarkacin bakinsa a nan kasar.

Daga jaridar almizan

Friday 1 April 2022

TIRKASHI,WASU FUSATATTUN MATASA SUN KONA MOTOCIN YAKIN NEMAN ZABEN SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA BISA ZARGINSA DA SA HANNU ACIKIN HARKAR RASHIN TSARON JIHAR

Wata sabuwa.....


Ana Zargin Sakataran Gwamnatin Jihar Katsina Kuma Dan Takarar Gwamna Dr. Mustapha Inuwa, Da Daukar Nauyin ‘Yan Ta’addan Dake Kai Hare-hare A Jihar Katsina


A jiya ranar Alhamis ne wasu fusatattun Matasa suka ƙone motar yankin Neman zaben Sakataren gwamnatin Jihar Katsina Kuma ɗan takaran gwamnan jihar a garin Charanci.


Lamarin ya auku ne a daida lokacin da a yarin motar Magoya bayan Sakataren gwamnatin suka zo wucewa ta garin na Charanci kan hanyar su ta zuwa karamar Hukumar Kankia domin halartar taron bayar da Tuta ga ƴan takarar Chiyamomi 34 na jam’iyyar APC.


Mustapha Inuwa, a baya baya ansha zarginsa da daukar nauyin ‘yan ta’addan dake kai hare hare a Jihar Katsina lamarin daya karyata Kuma yayi Bayanin alakarsa da ‘yan ta’addan Yan bindiga dake fa’din jihar ta Katsina.


A ranar 16 ga watan maris daya gabata ne sakataren Gwamnatin Jihar ta Katsina ya tara taron Yan jarida Kuma ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar Gwamnan jihar Katsina Kuma a lokacin yayi Bayanin alakarsa da ‘yan bindigar da ake Zargin sa a fadin jihar.


A lokacin da yake mayar da martani sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa, ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da ƴan bindiga kamar yadda ake ta raɗe-raɗin cewa wai yana da alakar kud da kud da ƴan bindiga a jihar, yace shima ya ɗanɗana azabar su kamar sauran mutane.


Inuwa wanda aka nada sakataren gwamnatin Katsina tun bayan zaman Aminu Masari gwamna ya bayyana aniyarsa na yin takarar gwamnan jihar a 2023.


Mutane da dama na zargin Inuwa da hada hannu da ‘yan bindiga da hakan ya sa matasa suka kona gidan sa dake karamar hukumar Danmusa a shekarar 2019.


Danmusa na daga cikin kananan hukumomin jihar Katsina da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga.


Ni ma na yi fama da hare-haren ‘yan bindiga, a cewar shi;


Yayin da yake ganawa da manema labarai ranar Laraba a lokacin da yake bayyana aniyar sa ta yin takarar gwamnan jihar Inuwa ya ba shi da alaka da ƴan bindiga fomin shima yayi fama da azabar da suka rika gallaza wa mutane, bai kubuta ba.


Ya ce sau biyu yana sadaukar da ransa domin a samu daidaituwa tsakanin gwamnati da ƴan bindiga kawai domin a samu zaman lafiya a jihar.


“A kan babur na yi dogon tafiya cikin gungurmin daji domin kawai a samu zaman lafiya. Na yadda su yi garkuwa da ni domin shugaban su ya je ya tattauna da gwamnati


“Na yi haka ne domin a samu zaman lafiya a jihar, kuma saboda na yadda da gwamna da kokarin da gwamnati ke yi don kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga a jihar.


“Ko su ‘yan bindigan sai da suka yi mamakin gani na a wannan lokacin.


Da yake bayanin yadda ya yi fama da hare-haren ‘yan bindiga Inuwa ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da babban wansa, ‘yar dan uwansa da abokinsa a Danmusa da dole sai da suka biya kudin fansa kafin aka sake su.


“Mukan zauna da ƴan bindigan da suka tuba duk bayan sati biyu domin tattaunawa da yadda za mu sasanta da sauran ‘yan bindigan.


“Sannan lokacin da maganan sasantawa da gwamnati ya rushe wasu daga cikin tubabbun ‘yan bindigan sun koma ruwa suna kai wa mutane hari.

MAL. NASIR EL-RUFA'I YAFITO YANUNAWA DUNIYA GAZAWAR GWAMNATINSU TA APC AKAN HARKAR TSARO TAREDA NEMAN GAFARAR AL'UMMAR NAJERIYA

 Mun Gaza A Matsayinmu Na Shugabanni Ku Yafe Mana ~ Gwamna El-Rufai Ya Roki Al-ummar Kaduna


Gwamnan Jihar Kaduna a Arewa maso yammacin Najeriya Nasir El-Rufai, ya nemi gafarar al'umma bisa hare-haren da 'yan bindiga da ke ci gaba da salwantar da rayukan a yankunan Jihar Kaduna, musamman harin da aka kai wa jirgin kasa a ranar Alhamis.


Gwamnan, wanda cikin yanayi mai cike da damuwa ya ce haƙiƙanin gaskiya yana cikin matuƙar bakin ciki saboda rabonsa da ya yi bacci tun ranar Alhamis, kuma ba ya iya bacci ko da ya sha maganin bacci saboda tsananin tashin hankali.


El-Rufa'i ya yi waɗannan kalamai ne lokacin da ya je karamar hukumar Giwa domin bai wa al'umma hakuri da ta'azziya da jaje bisa abubuwan da ke faruwa.


Ya kai ziyarar ne ranar Alhamis ƙarƙashin rakiyar mataimakiyarsa Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe da kuma wasu mukarraɓan gwamnatinsa.

Se dai wasu daga cikin matasan kasar najeriya suna ganin wannan ba'abin birgewabane don yafito yanuna gajiyawarsu,kamata yayi su sauka daga kan mukamansu gaba daya,daga cikin masu wannan ra'ayin akwai matashi kwararre akan harkar lafiya kuma mazaunin amerika dakta abdulaziz tijjani.


Sakon tuni ga yan najeriya daga sanata shehu sanii

 Ikon Allah,Babu irin zagin da ban sha ba,Babu irin cin mutuncin da ban gani ba a lokacin da muka fara magana kan rashin tsaro a Arewacin Na...